20/09/2026
GODIYA DA BAYANI GA AL'UMMAR SAFANA
Assalamu Alaikum.
Ina farin cikin sanar da al'ummar Safana cewa yau Asabar 20/09/2026 da misalin karfe 3:54 na yamma, mai girma Associate Professor Kamaluddeen Kabir Katsina, Coordinator na Katsina State Community Development Programme (CDP) ya gayyace ni domin jin cikakken bayani a kan korafin da muka gabatar dangane da rabon hatsin tallafi da ya gudana a ranar 14/09/2026.
Alhamdulillah, mun gaisa da shi cikin mutunci da girmamawa a Chamber ta Karamar Hukumar Safana, tare da 'yan Committee dinsa. Na gabatar masa da korafe-korafen al'umma yadda suke, kuma ya saurare ni sosai cikin natsuwa.
Muna matukar godiya gare shi bisa karamci da nuna kulawa da ya yi. Ya bani tabbacin cewa za su binciki lamarin sosai, kuma ya bani tabbacin cewa a gaba za a rika tuntubara a duk lokacin da za a yi wani rabon tallafi domin tabbatar da adalci da gaskiya.
Ni ma a nawa bangaren na tabbatar masa da cewa In Sha Allahu zan bada dukkan goyon baya da hadin kai wajen ganin an dakile duk wata almundahana a Safana.
Muna godiya ga hukumar CDP ta Jiha da ta saurare mu. Muna godiya ga al'ummar Safana da s**a goya baya da addu'a.
Adalci muke nema, kuma adalci In Sha Allahu zai tabbata.
Nagode.